Binciken ma’aunin yadda mutane ke kallon LGBTQI+ na F&M Global Barometers 2026
Barka da zuwa Binciken Ma’aunin Yadda Mutane ke kallon ‘Yancin Ɗan’adam kan LGBTQI+ na F&M Global Barometers 2026!
Wannan binciken an yi shi ne domin mutanen da suke bayyana kansu a matsayin LGBTQI+, waɗanda su ka haɗa da mata masu sha’awar mata da maza masu sha’awar maza da masu sha’awar jinsi guda da masu sha’awar jinsi biyu, masu sauya jinsi, masu bambancin jima’i, ko kuma masu halayen jinsi biyu, da sauransu. Zai ɗauki tsawon mintuna 2-5 kafin a kammala. Dukkannin amsoshin da za a bayar a tattaunawar za su kasance an sirranta su kuma an sakaya sunayen waɗanda suka bayar da amsoshin, daidai da ƙololuwar tsarin gudanar da bincike na ƙasa da ƙasa.
Mu, F&M Global Barometers, za mu so ku yi tunani game da abubuwan da kuka fuskanta masu alaƙa da ‘yancin ɗan’adam a matsayinku na LGBTQI+ a ƙasarku. Amsoshinku za su taimaka mana wajen fahimtar sauyin da ake samu game da ‘yancin ɗan’adam da suke da alaƙa da LGBTQI+ a faɗin duniya bayan lokaci. Za ku iya tura tambayoyi ko ƙorafi zuwa ga Dr. Susan Dicklitch-Nelson, Babban Mai Bincike a F&M Global Barometers, ta gbgr@fandm.edu.
Bincikenmu ya samu dubawa da amincewar hukumar tantancewa ta Institutional Review Board (IRB) da ke Franklin & Marshall College. Za a iya samun takardun amincewa bayan cikakken bayani A NAN. Za ku iya tura tambayoyi game da haƙƙoƙinku a matsayin masu halartar binciken zuwa ga Shugaba mai ci yanzu na IRB ta irb@fandm.edu.